Wasu jami’an ‘ƴan sanda masu ƙananan mukamai sun bukaci a jinkirta sabon tsarin ɗaukar aiki da rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ke shirin aiwatarwa, inda suka ce ya kamata a fara ba wa jami’an da ke aiki yanzu masu takardu dama ta haɓaka matsayin su bisa cancanta kafin a buɗe ƙofar sabbin daukar aiki.
A cikin wata wasika da suka aike wa da DCL Hausa a kungiyance, jami’an sun bayyana damuwarsu kan yadda rundunar ke shirin ɗaukar sabbin ma’aikata da ke da takardu irin su NCE, Diploma da Degree, alhali kuwa akwai ɗimbin jami’an da ke aiki yanzu waɗanda suka mallaki waɗannan takardu amma ba su samu karin girma ba.
“Mun bar makaranta domin yi wa ƙasa hidima, muna fatan za a yaba mana ta hanyar kara mana girma ko sauya mana matsayi bisa cancanta. Amma yanzu ana shirin ɗaukar sabbi daga waje, alhali mu muna nan muna aiki da gogewa,” in ji wasikar.
Jami’an sun ce rashin wanzar da wannan dama na iya karya kwarin guiwar ma’aikata da kuma rage nagartar aiki a cikin rundunar, musamman idan aka ci gaba da nuna halin ko in kula ga waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu tun da farko.
Sun bukaci DCL Hausa da ta:
• Bayyana damuwar su ga jama’a da hukumomi,
• Wayar da kai kan muhimmancin bai wa ma’aikatan da ke aiki dama ta ci gaba,
• Taimakawa wajen ƙarfafa adalci da ɗaga kwarin guiwar jami’an da ke aiki a halin yanzu.
DCL Hausa na ɗaya daga cikin kafafen da ke sa ido kan batutuwan da suka shafi adalci da walwalar ma’aikata, kuma za ta ci gaba da bibiyar wannan batu domin tabbatar da an ji murya daga cikin rundunar.
Idan kai ma kana da labari ko ƙorafi da ya shafi adalci a ma’aikata ko tsakanin al’umma, aiko mana da saƙon ka ta hanyar DCL Hausa Facebook ko email info@dclhausa.com
Kananan ‘yan sanda masu karatun NCE/Dilpoma/Degree sun roki a karbi takardunsu a kara musu girma
Recent Comments
on Gwamnatin Tinubu za ta fara ba da rancen maras kuɗin ruwa ga manoma da masu ƙananan sana’o’i – GEEP
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Jaridar Daily Trust ta gano dalilai uku da suka sa Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC na kasa
on Peter Obi ya sake jaddada bukatar kafa tsarin wa’adin shekara 5 kacal ga shugaban ƙasa a Najeriya
on Cire tsoffin ‘yan sanda daga daga tsarin Contributory Pension Scheme ya fi karfina – IGP Egbetokun
on Gwamnatin Nijeriya ta ɗage buɗe shafin neman aiki na Immigration, Civil Defence da sauran hukumomi
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An karkatar da Naira Bilyan 71.2 daga cikin Bilyan 100 na bashin dalibai a Nijeriya – Hukumar ICPC
on Gwamna Abba Gida Gida ya zabi tsohon shugaban ma’aikatansa da wasu mutum 5 a matsayin kwamishinoni
on Nijeriya za ta zama jagorar kasuwar halal ta duniya mai jarin Dala bilyan Dubu 7 – Kashim Shettima
