Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKasar Sierra Leone, ta karrama babban hafsan tsaron Nijeriya Olufemi Oluyede da...

Kasar Sierra Leone, ta karrama babban hafsan tsaron Nijeriya Olufemi Oluyede da lambar yabo

Shugaban ƙasar Sierra Leone, Julius Maada Bio, ya karrama babban hafsan tsaron Nijeriya CDS, Janar Olufemi Oluyede, da lambar yabo ta Grand Commander of the Order of the Rokel.

An ba Oluyede wannan lambar yabone a wani gagarumin faretin sojoji da aka gudanar, yayin gagarumin bikin sojoji da aka gudanar, kamar yadda daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya sanar a ranar Alhamis.

Baya ga karrama CDS na Nijeriya, an kuma bai wa wasu fitattun mutane daga Nijeriya, Guinea, Birtaniya, Amurka da Kenya lambobin yabo a wajen bikin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata