Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kaso 92 cikin 100 na ‘yan Nijeriya ba sa iya wanke hannu yadda ya kamata.
Jami’ar UNICEF ta jihar Borno,Dakta Marie Marcos, ce ta bayyana hakan a Larabar nan yayin bikin ranar wanke hannu ta shekarar 2025,inda tace samar da kayayyakin wanke hannu zai taimaka wajen inganta lafiyar al’umma baki daya.
Dakta Marcos ta bayyana cewa kashi 99 na ‘yan Nijeriya suna sane da lokacin da ya dace a wanke hannu, amma kashi 8 ne kawai ke iya yin hakan yadda ya kamata.
