Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiFiye da kashi 90 cikin 100 na iyaye mata a Najeriya na...

Fiye da kashi 90 cikin 100 na iyaye mata a Najeriya na shayar da jariransu -UNICEF

Babbar jami’ar kula da abinci mai gina jiki ta Hukumar UNICEF a ofishin Abuja, Nemat Hajeebhoy, ta bayyana jin dadinta kan yadda sama da kashi 90% na iyaye mata a Najeriya ke shayar da jariransu.

Ta bayyana haka ne ranar Juma’a yayin kaddamar da makon shayar da nono na duniya da aka gudanar a Ambursa, karamar hukumar Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ambato jami’ar ta na cewa shayar da jarirai ruwan nono ba kawai abinci ba ne, “rigakafi ne na farko ga jarirai kuma hanya ce ta dorewar rayuwa mai inganci ga yaran”

Ta kara da cewa duk da wannan adadi mai kyau, wasu sabbin bincike sun nuna raguwar shayar da ruwan nono na musamman (exclusive breastfeeding), don haka akwai bukatar hadin gwiwa daga dukkan masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa iyaye mata su cika wannan muhimmin aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata