Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cewa sama da kashi 75 cikin 100 na yara a jihar Katsina na fama da talauci ta fuskoki da dama, inda suke rasa muhimman abubuwan rayuwa kamar lafiya, abinci mai gina jiki, da ilimi.
Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ne ya bayyana haka a yayin taron horaswa na shugabannin kananan hukumomi 34 a jihar Katsina, wanda aka shirya don tattauna hanyoyin rage talaucin yara ta hanyar tsarin kariyar jama’a mai dogaro da sahihan bayanai.
Rahama ya bayyana cewa kididdigar hukumar kididdiga ta Nijeriya (NBS) da sauran hukumomi sun nuna cewa yawan mace-macen yara a jihar ya kai 159 cikin haihuwa dubu 1, wanda ke nufin yaro ɗaya cikin shida ba ya kai shekara biyar da rai.
Farah ya jaddada cewa zuba jari a kan yara wajibi ne, domin shi ne ginshiƙin da zai tabbatar da makoma mai ɗorewa da ci-gaba a jihar Katsina.
