Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaKiran kungiyar NNPYA na neman Tinubu ya zabe ni a takarar mataimaki...

Kiran kungiyar NNPYA na neman Tinubu ya zabe ni a takarar mataimaki a 2027 bai dace ba yanzu – Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau I. Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya ce kiraye-kirayen da kungiyar matasan jam’iyyar APC na Arewa (NNPYA) ke yi na a zabe shi a matsayin mataimakin Tinubu a 2027 ba su dace da lokaci ba.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Barau ya bukaci matasan su daina kamfen din su maida hankali kan tallafa manufar Shugaba Tinubu ta Renewed Hope Agenda ga Jama’ar kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito, mataimakin shugaban majalisar ECOWAS din ya ce, “Idan har kuna goyon bayana da gaske, ku daina wannan kiraye-kirayen da ba su dace ba, ku mara wa Shugaba Tinubu baya don dawo da martabar ƙasar nan.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata