- Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray, Okan Buruk, ya bayyana damuwarsa kan raunin da dan wasan gaba na Nijeriya Victor Osimhen ya samu yayin wasan da Super Eagles ta doke Rwanda da ci 1-0 a Uyo ranar Asabar.
Osimhen, wanda ke cikin jagororin tawagar Nijeriya da kuma kungiyar da yake buga wa wasa, ya ji ciwo a kafarsa wanda ya sa aka cire shi daga wasan.
Wannan ciwo ne ya hana shi halartar gagarumin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da Nijeriya za ta buga da Afirka ta Kudu a Talatar nan.
Buruk ya ce duk lokacin da Osimhen ke tafiya don wakiltar Nijeriya, suna cikin fargaba a Galatasaray.
A cewarsa ko yaushe suna cikin tsoron kada wani abu ya same shi, kuma a halin yanzu suna son aika jirgi nan take domin dawo da shi Turkiyya kamar yadda gidan jaridar Now Spor ya rawaito.
