Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotu a Abuja ta ba da damar a kama tare da tsare...

Kotu a Abuja ta ba da damar a kama tare da tsare wadanda suka tallata dandalin CBEX da ya wawure kudaden ‘yan Nijeriya

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, ta kama tare da tsare wasu masu tallata shafin kudin Crypto na CBEX da ake zargin ya wawure kudaden da suka haura dala biliyan 1 na ‘yan Nijeriya.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ba da umarnin ne, bayan ya saurari bayanai daga lauyar EFCC Fadila Yusuf.

Hukumar ta EFCC ta nemi izinin kotu domin ta kama wadanda ake zargin tallata wannan dandalin tare da tsare su, inda za ta ci gaba da bincike tare da shigar da kara.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata