Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotu a Nijeriya ta yi hukunci ga masu tayar da kayar baya...

Kotu a Nijeriya ta yi hukunci ga masu tayar da kayar baya 44

Manyan kotunan tarayya huɗu sun yanke wa ‘yan ta’adda 44 hukuncin dauri tsakanin shekaru 10 zuwa 30 tare da aiki mai wahala.

A cewar shugaban sashen yaɗa labarai na cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa, dake karkashin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Abu Michael, an yi wannan hukunci ne a tsakanin ranakun 9 zuwa 11 ga Yuli, 2025.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Michael ya ce waɗanda aka yanke wa hukuncin 44 na cikin mutum 54 da aka gurfanar a zagaye na 7 shari’ar gungun wadanda ake zargi da ta’addanci.

Ya ƙara da cewa sauran mutum 10 na jiran ci gaba da sauraren shari’ar su.

Zuwa yanzu, Nijeriya ta samu nasarar yanke jimillar hukunci 785 da suka shafi ta’addanci.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata