Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotu ta ba da belin Sanata Natasha kan Naira miliyan 50

Kotu ta ba da belin Sanata Natasha kan Naira miliyan 50

Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayar da belin Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan a kan kudi naira miliyan 50, bayan ta ki amsa laifin bata suna da ake zarginta da shi.

Kotun ta kuma ba da sharadin gabatar da mutum daya da zai tsaya mata wanda dole ne ya kasance mai gaskiya kuma ya mallaki kadarori a cikin Abuja.

Alkalin kotun Justice Chizoba Orji ya dage sauraren karar zuwa ranar 23 ga Satumba, 2025.

Tun da farko, gwamnatin tarayya ta gurfanar da ‘yar majalisar a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda uku da suka shafi bata sunan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata