Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKotu ta bayar da belin Yahaya Bello akan kudi Naira Milyan 500

Kotu ta bayar da belin Yahaya Bello akan kudi Naira Milyan 500

Yahaya Bello 

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta amince da bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan kudi Naira Miliyan 500 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya musanta tuhumar da ake masa na karkatar da naira biliyan 80 da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin zagon kasa ta EFCC ta yi masa.

An gurfanar da Bello a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya Abuja a kan tuhume-tuhume 19 na badakalar kudade.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata