Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiKotu ta dage zaman shari'ar DSS da Sowore

Kotu ta dage zaman shari’ar DSS da Sowore

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta dage zaman shari’ar da ake tuhumar dan gwagwarmaya a Najeriya Omoyole Sowore, sakamakon rashin gabatar da takardar tuhuma.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Umar ta tsayar da ranar 27 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraron karar.

Hakan ya biyo bayan da lauyan Sowore, Marshal Abubakar ya ce ba a gabatar musu da takardar tuhuma ba, sannan ba a samu wakilci daga bangaren manhajar X da ke cikin shari’ar ba, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Hukumar tsaron farin kaya DSS ce dai ta maka Sowore, kamfanin Meta da kuma manhajar X kotu, kan wasu kalaman sukar gwamnatin shugaba Tinubu da dan gwagwarmayar ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata