Kotun babban birnin tarayya ta Abuja ta rufe ma’aikata biyu na majalisar dokokin Nijeriya Mustapha Mohammed da Tijjani Goni a gidan yari, bisa kama su da laifin damfarar Naira miliyan 4.8 da sunan samar da aiki.
Mai Shari’a B.M. Bassi ne ya yanke wannan hukunci bisa samun su da laifin yaudarar mutane biyu da sunan za su sama musu aiki a babban bankin Nijeriya CBN da hukumar haraji ta FIRS.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ICPC, Demola Bakare ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa batun ya samo asali ne daga koke da wasu mutane suka shigar, wato Saifudeen Yakub da Aminu Abubakar, inda suka ce waɗanda ake zargin sun karɓi kuɗi don basu takardun bogi na aiki.
Bayan bincike, ICPC ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi haɗin baki da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.
