Monday, April 6, 2026
HomeKetareKotu ta daure wani dan Nijeriya a Amurka kan laifin zambar kudin...

Kotu ta daure wani dan Nijeriya a Amurka kan laifin zambar kudin gado

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Ehis Lawrence Akhimie hukuncin daurin shekaru fiye da takwas bayan an same shi da laifin zamba.

Ofishin Lauyan Gwamnatin Amurka na Southern District of Florida ya bayyana a ranar Litinin cewa Akhimie, mai shekara 41, an yanke masa hukuncin watanni 97 a kurkuku a ranar 11 ga Satumba, bayan ya amsa laifin haɗa baki wajen aikata wannan zamba.

Bisa bayanan kotu, Akhimie da abokan aikinsa sun aike da takardu na bogi ga ‘yan kasar ta Amurka suna yi musu karyar cewa jami’an banki ne daga kasar Spaniya.

A cikin wasikun, sun yi ikirarin cewa wadanda aka turo musu suna da hakkin karɓar gadon makudan kudi daga dangin su da suka ce sun mutu a ƙasashen waje.

Sai dai kuma rahoton jaridar Punch ya nuna cewa, kuɗaɗen duk an karkatar da su ta hanyar cibiyar masu shiga tsakani, ciki har da tsofaffin waɗanda ma kansu sun taba zama ƙorarrun masu zamba a Amurka, inda aka yaudare su su karɓi kuɗaɗen sannan su miƙa ga masu aikata laifin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata