Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKotu ta gayyaci Akpabio, Nwaebonyi kan take hakkin Natasha

Kotu ta gayyaci Akpabio, Nwaebonyi kan take hakkin Natasha

Wasu manyan kotuna a Abuja guda biyu sun gayyaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da Sanata Onyekachi Nwaebonyi, bisa zargin bata suna, cin zarafi, da kuma take hakkin sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

A karar mai lamba FCT/HC/CV/754/2025 a gaban mai shari’a Abubakar Idris Kutigi, kotun ta ba Akpoti-Uduaghan izinin mika takardar sammaci da duk wasu matakai da suka hada da sauraran karar da Sanata Akpabio,da Sanata Onyekachi, cikin sammacin akwai babban mai taimaka wa Akpabio, Mfon Patrick, da magatakardar Majalisar dattawa.

Mai shari’a Kutigi ya sanya ranar 9 ga watan Yuni, 2025, domin sake yin zama kan shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata