Mai shari’a James Omotosho da ke babbar kotun tarayya da ke Abuja ya kori karar da aka shigar, ta neman sahihancin dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya.
Mai shari’a Omotosho ya dauki matakin ne bisa ga yadda ya ce masu shigar da kara ba su da hurumin kai wa gaban kotu.
Channels TV ya wallafa cewa, masu karar sun kai lamarin gaban kotun ne, suna neman ta haramta dakatarwar da majalisar dattawan ta yi wa Sanatar, wadda tun da fari aka zarge ta da karya ka’idoji da kin bin doka.
