Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar binciken ingancin takardar shaidar sakandare ta Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Mai shari’a Binta Nyako ce ta bayar da izinin bayan bukatar da wani mai fafutuka, Emorioloye Owolemi, ya shigar ta hannun lauyansa, SAN Philemon Yakubu, bisa Dokar ‘Yancin Samun Bayani ta 2011.
Bukatar na neman a binciki sahihancin takardar WAEC da ministan ya gabatar. Kotun ta amince da a ci gaba da sauraron shari’ar, inda ta sanya ranar 14 ga Maris domin ci gaba da zama kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai wata kotun tarayya daban karkashin Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ki amincewa da wata bukata ta daban wadda ke neman binciken takardar kammala yi wa kasa hidima ta NYSC ta ministan.
A cikin waccan bukata, mai karar ya nemi a tilasta wa NYSC ta bayar da bayanai kan takardun hidimar ministan, ciki har da bayanan rajista da biyan alawus, amma kotun ta yi watsi da rokon.
