Kotun ta yanke hukunci ga tsohon shugaban kasar Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yoel ne a ranar Alhamis, bayan samunsa da laifin jagorantar yunƙurin tayar da bore ta hanyar ayyana dokar ta-ɓaci a shekarar 2024.
Yoon ya bayyana dokar ta-ɓaci ne kwatsam a wani jawabi da yayi a gidan Talabijin a watan Disambar 2024, inda ya ce akwai buƙatar ɗaukar tsauraran matakai domin kawar da ƙungiyoyin da ke adawa da ƙasa a majalisar dokokin ƙasar.
Tsohon shugaban mai shekaru 65, wanda aka tube daga muƙaminsa, daga bisani aka kama shi tare da gurfanar da shi a kan jerin tuhuma da suka haɗa da tayar da bore da hana aiki ga hukumomin shari’a.
Alkalin da ya jagoranci shari’ar, Ji Gwi-yeon, ya ce Yoon ya tura sojoji zuwa ginin majalisar dokoki ne domin murƙushe abokan hamayyarsa na siyasa, waɗanda ke hana shi aiwatar da manufofinsa.
