Monday, April 6, 2026
HomeKetareKotun a Faransa ta daure tsohon shugaban kasar shekaru biyar a gidan...

Kotun a Faransa ta daure tsohon shugaban kasar shekaru biyar a gidan yari

Wata kotu a birnin Paris ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Faransa, Nicolas Sarkozy, hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ranar Alhamis, bayan ta same shi da laifin haɗin baki wajen karɓar kuɗaɗen haram daga gwamnatin tsohon shugaban Libiya, Moammar Gadhafi, domin ya tallafa masa a yaƙin neman zabe.

Kotun ta tabbatar da samun sa da laifin samun tallafin kuɗi daga Libiya daga shekarar 2005 zuwa 2007. Sai dai ta wanke shi daga wasu tuhumce-tuhumce guda uku, ciki har da cin hanci da kuma ɓoye kudaden gwamnati.

Sarkozy, wanda yanzu yake da shekaru 70, ya musanta laifin a tsawon shari’ar da ta ɗauki watanni uku, inda ya bayyana cewa makarkashiya ce ta siyasa ake shirya wa kansa.

Sarkozy, wanda aka zaɓa a shekarar 2007, ya sha kaye a 2012, har yanzu yana da tasiri a siyasar kasar ta Faransa duk da jerin shari’o’in da suka yi masa katutu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata