Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa wasu ‘yan Nijeriya biyar hukuncin daurin shekara 159 a gidan yari bisa samunsu da laifin damfarar Amurkawa, kamfanoni da hukumomin gwamnati sama da 100 kudaden da suka kai dala miliyan 17.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jaridar Punch ta samu a shafin yanar gizo na ma’aikatar shari’a ta Amurka a ranar Laraba, mai dauke da sa hannun mukaddashin babban lauyan Amurka na gundumar Gabashin Texas, Ray Combs.
Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake tuhumar, Damilola Kumapayi, Sandra Iribhogbe, Edgal Iribhogbe, Chidindu Okeke da Chiagoziem Okeke, na cikin wani gungun ‘yan damfara na kasa da kasa
Lauyan ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun fara wannan harkalla ne a shekarar 2017 ta hanyar damfarar tsofaffi.
