Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKotun Ghana ta yanke wa ’yan Nijeriya uku hukuncin daurin shekaru 96...

Kotun Ghana ta yanke wa ’yan Nijeriya uku hukuncin daurin shekaru 96 kan satar motoci

Wata kotu a Ghana ta yanke wa wasu ’yan Nijeriya uku hukuncin zaman kurkuku na shekaru 96 kowannen su bisa laifin satar motoci a birnin Kumasi.

An kama mutanen ne a ranar 20 ga Yuni, 2025, bayan an zargesu da satar motocin da aka yi a cikin birnin.

Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan karuwar aikata laifuka da ake zargin baki suna yi a ƙasar.

A watan Yuli dai, hukumar shige da fice ta Ghana ta kama ’yan Nijeriya 50 a Accra bisa zargin damfara ta yanar gizo da kuma fataucin mutane zuwa kasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata