A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta yanke, ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara da ke Abuja, wadda ta amince da Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na kasa.
Kotun kolin ta ce kotun daukaka kara ba ta da hurumin sauraren karar, ganin cewa lamarin cikin gida ne na jam’iyyar.
Kotun ta jaddada cewa al’amuran jam’iyya na cikin gida, bangaren shari’a ba shi da hurumin saurarensa.
