Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da ake zargin Manjo...

Kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da ake zargin Manjo Al Mustapha da hannu wajen halaka matar Abiola

Kotun Kolin Nijeriya ta yi watsi da shari’ar da aka shigar da Manjo Hamza Al Mustapha, kan zarginsa da hannu wajen halaka Kudirat Abiola, matar marigayi Cif MKO Abiola.

Gidan talabijin na NTA ya bayyana cewa rahoton shari’ar ya nuna kwamitin alkalai biyar na kotun kolin karkashin jagorancin mai Shari’a Uwani Aba-Aji, ta yanke hukunci a kan shari’ar da Gwamnatin jihar Legas ta shigar tun da fari.

Kotun ta ce Gwamnatin jihar Legas ta nuna rashin kulawa kan shari’ar da aka dauki shekara da shekaru ana gudanar da ita.

Kotun Koli ta kuma nuna takaicinta kan yadda Gwamnatin Legas ta kasa tura wakilci ko lauyanta, duk da cewa an aika mata da sanarwar zaman shari’a tun shekarar 2020, kuma ba a gabatar da wani bayani ga kotu ko bangaren da ake kara ba, saboda haka, kotun ta yanke hukuncin korar shari’ar gaba daya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata