Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa matsalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu na wucin gadi ne, yana mai cewa akwai kyakkyawar makoma a gaba karkashin manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Shettima ya bayyana hakan ne a sakon bikin Easter da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, inda ya jaddada kudurin gwamnati na samar da zaman lafiya, farfado da tattalin arziki da kuma bunkasar kasa a dogon lokaci.
Ya ce duk da wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, kasar ba ta taba rushewa saboda kalubale ba, yana mai nuna kwarin gwiwa cewa hadin kai da sadaukarwa za su taimaka wajen shawo kan matsalolin.
