Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKudin da aka ba Super Falcons zai iya biyan albashin likitoci 16,000...

Kudin da aka ba Super Falcons zai iya biyan albashin likitoci 16,000 da malamai 66,000 – Rahoton Daily Trust

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa kuɗin da aka bai wa ƴan wasan ƙungiyar mata ta Nijeriya Super Falcons, bayan nasararsu a gasar WAFCON 2024, ya kai adadin da zai iya biyan albashin fiye da likitoci 16,000, malamai 66,000, da kuma fiye da ‘yan sanda 78,000 da ke matakin albashi mafi ƙasa, na wata guda.

Rahoton ya jaddada cewa a lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin rashin isasshen albashi da yin ƙaurar likitoci zuwa ƙasashen waje, wasu ma’aikatan lafiya a wasu jihohi na karɓar ƙasa da Naira 250,000 a wata, duk da cewa suna fuskantar barazana ga rayuwarsu wajen ceton jama’a.

Gwamnatin Tinubu da kungiyar gwamnonin kasar dai sun fitar da Naira biliyan 4.95 a matsayin lada ga ƴan wasa da masu horar da su, tare da bai wa kowanne gida mai ɗakuna uku a sabon shirin gidaje na “Renewed Hope Estate”.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata