Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKungiyar CONUA ta nesanta kanta da yajin aikin malaman jami’a ta ASUU

Kungiyar CONUA ta nesanta kanta da yajin aikin malaman jami’a ta ASUU

Kungiyar malaman jami’a ta CONUA ta bayyana cewa ba ta cikin yajin aikin da kungiyar ASUU ke gudanarwa a fadin ƙasar nan.

Shugaban kungiyar, Farfesa Niyi Sunmonu, ya musanta rahotannin da ke cewa kungiyar na cikin yajin aikin.

Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa CONUA ta kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da daidaito a harkokin ilimi ta hanyar tattaunawa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani dalili da zai sa reshen na CONUA ya shiga yajin aiki, tare da jan hankalin mambobinsu su ci gaba da gudanar da ayyukansu na koyarwa da gudanarwa yadda ya kamata.

Farfesa Sunmonu ya kara da cewa reshen kungiyar ya taba kokawa kan cire su daga kwamitin sake nazarin yarjejeniyar 2009 tsakanin malaman jami’a da gwamnatin tarayya, amma daga bisani ma’aikatar ilimi ta fadada kwamitin kamar yadda ta yi alkawari, don haka babu wani hujja na yajin aiki daga CONUA.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata