Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiKungiyar direbobin man fetur ta goyi bayan Dangote tare da caccakar matakin...

Kungiyar direbobin man fetur ta goyi bayan Dangote tare da caccakar matakin NUPENG na shiga yajin aiki

Direbobin tankokin man fetur na ƙungiyar PTD sun yi watsi da sanarwar yajin aiki da ƙungiyar NUPENG ta fitar kan zargin cewa kamfanin Dangote ya hana direbobin motocin iskar gas (CNG) shiga ƙungiyoyin ƙwadago.

A baya NUPENG ta ce ma’aikatanta za su daina aiki daga ranar 8 ga Satumba tare da fara neman wasu ayyuka.

Sai dai wakilan PTD na yankin Warri, Blessing Dafinone, da na yankin Port Harcourt, Joseph Dagogo-Jack, sun ce ba za su bi wannan umarni ba, suna mai kiran matakin a matsayin “abin da ba za a lamunta da shi ba.”

Sun soki ƙungiyar NUPENG bisa gazawarta wajen neman tattaunawa ko sulhu kafin sanar da yajin aiki, inda suka jaddada cewa ƙungiyoyin ƙwadago ya kamata su kasance masu ɗaukar nauyin al’umma ba wai masu neman moriyar kansu ba, domin kuwa matakansu na iya kawo cikas ga cigaban tattalin arzikin ƙasa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata