Tuesday, April 7, 2026
HomeKetareKungiyar ECOWAS za ta yi wani taro a Ghana kan ficewar kasashen...

Kungiyar ECOWAS za ta yi wani taro a Ghana kan ficewar kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS za ta yi wa k taro a Ghana a Talatar nan domin tattaunawa kan ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.

Taron dai zai gudana a tsawon kwanaki biyu, kamar yadda wata sanarwar kungiyar ta nuna.

ECOWAS ta ce kasashe mambobin kungiyar za su tattauna kan tasirin ficewar kasashen ga hukumomin ECOWAS.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa a shekarar da ta gabata ne kasashen uku da ke karkashin mulkin soja suka fice daga kungiyar a hukumance.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata