Kungiyar Kare Hakkin Dan’Adam ta nemi a sauya ranar tantance ’yan sanda saboda Ramadan
Kungiyar kare hakkin dan’Adam ta kasa da kasa (IHRC-RFT) ta bukaci a sake duba ranar tantance masu neman aikin dan sanda 50,000 da hukumar ‘yan sanda da rundunar ‘yan sandan Nijeriya suka shirya fara yi a ranar 9 ga Maris, 2026, sakamakon zuwan hakan daidai da watan Ramadan.
Kungiyar ta ce ta samu koke daga masu neman aikin cewa azumin Ramadan na iya jefa su cikin wahala, duba da irin gwajin jiki da ake yi a tantancewar. Ta roki shugabannin hukumomin tsaro da kwamitocin majalisa da su duba yiwuwar dagewa zuwa bayan Ramadan domin tabbatar da adalci da daidaito.
Kungiyar ta ce irin wannan mataki zai nuna girmama bambancin addini da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki kan daidaito da kare hakkokin jama’a.
