DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiKungiyar kwadago a Nijeriya NLC ta yi barazanar daukar mataki idan har...

Kungiyar kwadago a Nijeriya NLC ta yi barazanar daukar mataki idan har gwamnati ba ta janye dokar ta ɓaci a Rivers ba

 

Kungiyar Kwadago a Nijeriya ta yi Allah wadai da kakaba dokar ta baci a jihar Rivers, ta kuma yi barazanar daukar mataki idan har gwamnati ba ta janye dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan gargadi ya fito ne daga cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka hada da kungiyar kwadago reshen jihar Rivers Alex Agwanwor da shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Ikechukwu Onyefuru da wasu kungiyoyi suka sanyawa hannu.

A cewar shuwagabannin kungiyoyin al’ummar jihar Rivers sun fito sun zabi wadanda suke so su shugabancesu sabi da haka duk wani yunkuri na dakatar da su, ba tare da bin tsarin mulkin kasa ba yana kawo cikas ga dimokradiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata