Monday, April 6, 2026
HomeWasanniKungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sallami mai horaswarta Igor Tudor

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sallami mai horaswarta Igor Tudor

Kungiyar Juventus ta sallami kocinta Igor Tudor a ranar Litinin bayan shan kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, wanda ya sa kungiyar ta tara maki biyar kacal a wasanni biyar da suka gabata.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito kungiyar ta sanar da cewa Massimiliano Brambilla zai jagoranci tawagar a wasan da za su fafata da Udinese ranar Laraba.

A cikin sanarwar, Juventus ta gode wa Tudor da tawagarsa bisa jajircewa da ƙwarewar da suka nuna tun lokacin da ya karɓi ragamar horaswar a watan Maris.

Juventus tana matsayi na takwas a gasar Serie A, maki shida a bayan Napoli, kuma ba ta lashe wasa ba tun ranar 10 ga Satumba ba, tana da jerin wasanni takwas ba tare da nasara ba.

Jimillar aikinsa a kungiyar, Tudor a Juventus ta kasance nasarori 10, canje 8, da rashin nasara 6, duk da kashe euro miliyan 130 wajen siyan sababbin ‘yan wasa a lokacin bazara.

Tudor, tsohon ɗan wasan tsakiyar ƙasar Croatia mai shekaru 47, ya taba buga wa Juventus wasa a lokacin da yake taka leda, kafin daga baya ya karɓi aikin horaswa daga hannun Thiago Motta a watan Maris.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata