Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKungiyar likitoci a Nijeriya za ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyar likitoci a Nijeriya za ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani

Kungiyar likitoci a Nijeriya NARD ta ayyana tsunduma yajin aiki daga ƙarfe 11:59 na dare ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025, saboda gaza biyan bukatun da ta gabatar ga gwamnatin tarayya.

Kamar yadda sanarwar kungiyar ta nuna a ranar Asabar, Shugaban NARD, Dakta Mohammed Usman Suleiman, ya bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan taron gaggawa na awanni biyar da kwamitin zartarwa na ƙasa ya gudanar.

Ya ce umarnin shiga yajin aikin ya biyo bayan cika wa’adin kwanaki 30 da kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya domin ta biya bukatunta, amma har yanzu babu wani mataki da aka dauka.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata