Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya ta soki shirin...

Kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya ta soki shirin Dangote na kai man fetur kai tsaye ga gidajen mai a kasar

Ƙungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya ta nuna rashin amincewa da shirin Dangote Refinery na fara raba kayayyakin man fetur kai tsaye zuwa gidajen mai a fadin ƙasar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar na ƙasa, Joseph Obele, ya fitar a ranar Litinin, PETROAN ta bayyana cewa wannan tsari na iya zama barazana ga ‘yan kasuwa da ke harkar man fetur a matakin ƙasa, tare da haifar da matsin lamba ga ayyukan yi a fannin.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar, Dangote Refinery dai ta sanar da shirin faɗaɗa rabon man fetur zuwa manyan gidajen mai a fadin ƙasa a ƙarshen mako da ya gabata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata