Kungiyar
matan jami’an ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta raba awaki 137 ga
matan da mazajensu suka mutu da kuma marasa galihu, domin bunkasa rayuwarsu
Hakan
dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan
sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano.
Shugabar ƙungiyar
Aisha Gumel wacce kuma ita ce uwargidan kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta ce
matakin wani aiki ne na yau da kullun na tallafawa iyalan ma’aikatan da suka
mutu da waɗanda sukai ritaya da sauran marasa galihu a cikin al’umma.
Aisha
ta gabatar da takardar shaidar koyon sana’o’i ga ‘yan kungiyar sama da 100 da
suka samu horo tare da daukar nauyin fara sana’o’i daban-daban daga kungiyar.

