Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiKungiyar Sanatocin Arewa ta yi tir da kisan da aka yi wa...

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi tir da kisan da aka yi wa wasu matafiya 12 da suka fito daga jihar Kaduna

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da ajalin matafiya 12 ‘yan jihar Kaduna da wasu suka yi a jihar Filato yayin da suke tafiya daurin aure a karamar hukumar Pan da ke jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar Litinin dinnan, Shugaban kungiyar Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, ya bayyana harin a matsayin rashin rashin imani, yana mai jaddada cewa irin wannan mummunan tashe-tashen hankula na bukatar gaggauta yin abinda ya dace a kansu.

Ya jaddada cewa irin wannan kisa na rashin hankali da ake yi wa ‘yan kasa wayanda ba su ji ba ba su gani ba, abu ne da ba za a amince da shi ba, don haka akwai bukatar a dauki matakin gaggauwa dan kaucewa ci gaba da faruwar hakan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata