Kungiyoyin ƙwadago a Nijeriya, NLC da TUC, sun ce matakin nasu ya biyo bayan wani kudiri da suka cimma a wani taro da ya gudana ranar 6 ga watan Agusta.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Peter Jediel, da shugaban TUC, Sule Abasu, suka sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, yajin aikin na zuwa ne a matsayin martani ga wasu kura-kurai da kwamitin da ke kula da bayanan jihar ya yi, wanda shugabannin ƙwadago ke cewa ya yi wa ma’aikatan jihar illa.
Sun zargi kwamitin da aikata laifukan da suka saba wa doka, tare da zargin gwamnatin jihar da rashin yin abin da ya dace kan wa’adin da aka ba su a baya na yin duk abin da ya dace ga ma’aikatan jihar.
