Babban sakatare a ofishin kula da ayyukan magudanar ruwa da albarkatun ruwa a jihar Legas, Mahmood Adegbite, ya ce mutanen da ke hakar rijiyar burtsatse a yankin Lekki na jihar wata kila suna shan ruwan bahaya.
Da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a jihar, Adegbite ya bayyana cewa gurbacewar rijiyoyin burtsatse a Lekki na da illa ga lafiyar al’umma.
Ya ce, ya kamata a kawar da duk wata cuta da za ta iya haifar da sakamakon rashin lafiyar al’umma, ya kara da cewa gwamnati ta yi kokarin magance matsalar ambaliyar ruwa.
