Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya jagoranci taro da shugabannin jam’iyyar a jihar Cross River domin tsara dabarun fuskantar babban zaben 2027.
Taron, wanda aka gudanar a Calabar ranar Talata, ya tattaro manyan mambobin jam’iyyar daga sassan jihar, inda aka tattauna batun ƙarfafa jam’iyya da kuma samar da hadin kai.
Da yake jawabi, Kwankwaso ya yaba da irin gudunmawar da aka bayar a zaben 2023, tare da jaddada cewa cimma nasara a 2027 na bukatar haɗin kai da jajircewa.
Ya karfafesu da su ci gaba da dagewa wajen tabbatar da haɗin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar, a cewarsa wannan shi ne sirrin nasarar jam’iyya a matakin jiha da kuma ƙasa baki ɗaya.
