Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa suna nan daram a jam’iyyar ADC, yana mai cewa ba su da niyyar ficewa zuwa kowace jam’iyya.
Kwankwaso ya ce duk wani yunkuri da Nafiu Bala ke yi na haddasa rikici a cikin jam’iyyar ADC ba zai yi nasara ba.
Ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu da amfani da Nafiu Bala domin hada husuma da kuma rage tasirin ADC.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanta wa da DCL Hausa kan makomar siyasar jam’iyyar ADC da adawa a kasar.
A cewarsa, maimakon hakan ya rage musu ƙarfi, sai ƙara musu ƙwarin gwiwa tababar ke yi.
Kwankwaso ya ƙara da cewa aikin gwamnatin Tinubu bai gamsar da ‘yan Najeriya ba, yana mai cewa jama’a sun riga sun yi watsi da APC.
