Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaLakurawa sun yi ajalin makiyaya goma a jihar Kebbi

Lakurawa sun yi ajalin makiyaya goma a jihar Kebbi

Aƙalla makiyaya goma ne aka ruwaito sun rasu a harin ramuwar gayya da aka kai wa Fulanin kauyen Tilli da ke Ƙaramar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.

Rahotanni da jaridar Daily Trust ta tattaro sun bayyana cewa bayan ajalin ɗan sa-kain, mutane suka kai hari kan wasu Fulanin yankin, inda aka dauki ran akalla mutane goma a cikin mamayar da aka yi wa sansanoninsu.

Ya ƙara da cewa Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na kasa (MACBAN) tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, sun ziyarci yankin domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin.

Da aka tuntubi Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba tukuna.

Sai dai ya yi alkawarin binciko gaskiyar lamarin da dawo da bayani, amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata