Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiLegas ce cibiyar kasuwancin Nijeriya - Martanin Daniel Bwala ga masu sukar...

Legas ce cibiyar kasuwancin Nijeriya – Martanin Daniel Bwala ga masu sukar manyan ayyukan gwamnatin tarayya a jihar

Mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai Daniel Bwala, ya ce jihar Legas ta kowa ce, sannan ta kasance alfaharin tattalin arziƙin kasar.

A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Laraba, Bwala ya ce mayar da hankalin gwamnatin tarayya wajen aiwatar da manyan ayyuka a Legas ba son kai ba ne, illa dai saka jari ne a cibiyar kasuwancin ƙasar.

A cewarsa attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Dangote dan Arewa ne, amma kasuwancinsa yana Legas, kuma dukkan manyan masu kudi a Najeriya suna da jari a jihar.

Bwala ya kwatanta Legas da biranen kasuwanci na duniya irin su London, New York da Paris, inda ya ce cibiyar tattalin arziƙin ƙasa na samun mafi yawan ayyukan gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata