Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiLimamin da ya ceci Kiristoci 262 lokacin rikicin addini a jihar Plateau...

Limamin da ya ceci Kiristoci 262 lokacin rikicin addini a jihar Plateau ya rasu

Limamin garin Nghar da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Plateau, Abubakar Abdullahi, wanda ya shahara da ceton Kiristoci 262 a rikicin addini na 2018, ya rasu yana da shekara 90.

Ɗansa, Saleh Abubakar, ya tabbatar wa Daily Trust cewa mahaifinsa ya rasu ne a daren Alhamis a Asibitin Kwararru na Plateau da ke Jos, bayan kwana goma da kwantar da shi sakamakon ciwon zuciya da ya dade yana fama da shi.

Marigayin ya bar ’ya’ya 19, maza 12 da mata bakwai. Za a yi jana’izarsa ne a yau Juma’a bayan sallar Juma’a a garin Nghar.

A watan Yunin 2018, yayin rikicin addini da ya shafi kauyuka 10 a Barkin Ladi, Limamin ya boye Kiristoci 262 a masallaci da gidansa har rikicin ya lafa, lamarin da ya ceci rayukansu. Saboda wannan jarumta, ya samu lambobin yabo da dama, ciki har da International Religious Freedom Award daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a 2019.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata