Tuesday, April 7, 2026
HomeWasanniLiverpool ta yi cefanen 'yan wasa na sama da Euro milyan 250...

Liverpool ta yi cefanen ‘yan wasa na sama da Euro milyan 250 a kakar wasa mai zuwa

Liverpool ta fara shirya wa kare kambinta a gasar Premier League ranar Juma’a, 15 ga Agusta da Bournemouth a Anfield.

Kungiyar ta sabunta tawagarta da sabbin ‘yan wasa ciki har da Florian Wirtz Yuro miliyan 116.5, Hugo Ekitike, Jeremie Frimpong, Milos Kerkez da Mamardashvili, a karkashin kocin Arne Slot.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka bar kulob din sun hada da Trent Alexander-Arnold (Real Madrid), Luis Díaz (Bayern Munich), da Darwin Núñez wanda ke nazarin barin kulob din.

Slot zai ci gaba da amfani da tsarin 4-2-3-1 da ya kawo nasara bara, inda sabbin ‘yan wasan za su taka muhimmiyar rawa. Kulob din na fatan kare kambinsa bisa karfin da sabbin sauye-sauyen suka samar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata