Thursday, April 9, 2026
HomeSiyasaLokaci ya yi da Najeriya za ta daina karbar agajin lafiya daga...

Lokaci ya yi da Najeriya za ta daina karbar agajin lafiya daga ketare – Majalisar Tarayya

Majalisar tarayyar Nijeriya ta ce lokaci ya yi da kasar za ta daina karbar tallafin lafiya daga ketare, inda ta sanar da shirin fara ɗaukar nauyin lafiyar jama’arta da kanta.

Wannan ya biyo bayan da aka yanke kaso 11 na kudaden tallafi da asusun lafiya na duniya ke bai wa kasar, wanda adadin sa ya kai dala miliyan 100, sakamakon kalubalen kudi da ake fuskanta a fadin duniya, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Yayin bikin bude taron tattauna hanyoyin ciyar da Nijeriya gaba karo na 70 da aka gudanar a jihar Legas, babban jami’in da ke kula da asusun lafiya na duniya a Nijeriya Jean- Thomas Nouboussi, ya bukaci gwamnatin kasar ta bullo da wasu hanyoyin samun kudin shiga don cike gibin da aka samu a fannin na lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata