Shugabar shirin AGILE a Jihar Kaduna, Maryam Sani Dangaje, ta yi kira ga iyaye da su daina dorawa ‘ya’yansu mata talla, su maida hankali wajen saka su makaranta domin neman ilimi da inganta rayuwarsu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugabar ta bayyana hakan ne yayin yakin wayar da kai da fadakarwa na Ma’aikatar Ilimi ta Kaduna, karkashin shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE), wanda Bankin Duniya ke daukar nauyi.
A cewarta, dora wa ‘ya mace talla babban kalubale ne ga rayuwarta, domin yana iya jefa ta cikin hadurran cin zarafi da sauran matsaloli na rayuwa.
