Luka Modric zai koma kungiyar kwallon kafa ta AC Milan bayan kammala gasar Club world cup
Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric, wanda zai cika shekaru 40 a watan Satumba, na iya barin kulob din bayan dogon lokaci.
Modric ya koma Real Madrid daga Tottenham a shekarar 2012, kuma tun farkon watan Yuni ake danganta shi da yiwuwar komawa gasar Serie A ta Italiya kamar yadda rahoton gidan talabijin na Channels ya tabbatar.
