Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiMa'aikatan da matatar Dangote ta dakatar za su koma bakin aikinsu -...

Ma’aikatan da matatar Dangote ta dakatar za su koma bakin aikinsu – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Nijeriya ta ce kamfanin Dangote zai mayar da ma’aikatan da matatarsa ta dakatar biyo bayan samun sabani tsakanin ta da kungiyar PENGASSAN.

Ministan kwadago, Dr Mohammed Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce za a biya ma’aikatan hakkokinsu ba tare da rage musu ko kwabo ba.

Haka kuma ya kara da cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya yayin da kungiyar PENGASSAN ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin da ta tsunduma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata