Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMa’aikatan gwamnati na amfani da kuɗin sata wajen gina gidaje a Abuja...

Ma’aikatan gwamnati na amfani da kuɗin sata wajen gina gidaje a Abuja – EFCC

Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce yawancin gidajen da aka yi watsi da su a babban birnin tarayya Abuja mallakar ma’aikatan gwamnati ne da suka sace dukiyar al’umma.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba yayin wani taron tattaunawa, inda yake bayyana cewa an yi watsi da wasu kadarori fiye da shekaru goma.

Shugaban na EFCC ya ce hukumar ta kafa wata tawaga ta musamman da za ta fara ziyartar irin waɗannan wuraren da kadarorin suke.

Shugaban ya ce abin mamaki shi ne mafi yawan waɗannan gidaje mallakar ma’aikatan gwamnati ne da suka sace kuɗaɗe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata