By Salamatu Alhassan Musa
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tana kan kudurinta na biyan ragowar watanni uku na tallafin Naira 35,000 ga ma’aikatan gwamnati, ba tare da wani jinkiri ba.
Daraktan Sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Bawa Mokwa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, Juma’a, 8 ga watan Agusta, shekarar 2025.
Mokwa ya ce an riga an biya kaso na biyu na tallafin, inda yanzu saura watanni uku a kammala biyan ƙarin albashin.
