Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMa'aikatar tsaron Nijeriya na bukatar ƙwararren shugaba - Shehu Sani

Ma’aikatar tsaron Nijeriya na bukatar ƙwararren shugaba – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawan Nijeriya da ya wakilci Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya nuna bukatar samun ƙwararren shugaba da zai jagoranci ma’aikatar tsaron Nijeriya.

 

Kalaman tsohon dan majalisar sun zo ne bayan da ministan tsaron Nijeriya Badaru Abubakar ya sanar da yin murabus sakamakon dalilai na lafiya kamar yadda fadar shugaba Tinubu ta tabbatar.

 

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya ce a daidai wannan lokaci da kasar ke fuskantar ta’azzarar matsalar tsaro a sassa daban daban, ya zama wajibi Nijeriya ta iya kare kanta daga hare-haren ‘yan ta’adda, wanda samun kwararre ne kadai zai kai ga iya cimma wannan nasara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata